Episode's summary
A wannan makon shirin ya yi nazari kan yadda tsadar maganin asibiti ke tilastawa jama’a karkatawa amfani da magungunan gargajiya, kodayake akwai kiraye-kirayen masana game da illar waɗannan magunguna a mahangar likitanci. A ƙasashe irin Najeriya magungunan na gargajiya na matsayin hanyoyin neman waraka wanda aka gada tun kaka-da-kakanni kuma aka yi amanna da tasirinsu, duk kuwa da kiraye-kirayen ƙaurace masa dama ƙorafe-ƙorafe kan illolinsa nan da can, musamman daga likitoci da sauran jami’an lafiya.
A wannan makon shirin ya yi nazari kan yadda tsadar maganin asibiti ke tilastawa jama’a karkatawa amfani da magungunan gargajiya, kodayake akwai kiraye-kirayen masana game da illar waɗannan magunguna a mahangar likitanci. A ƙasashe irin Najeriya magungunan na gargajiya na matsayin hanyoyin neman waraka wanda aka gada tun kaka-da-kakanni kuma aka yi amanna da tasirinsu, duk kuwa da kiraye-kirayen ƙaurace masa dama ƙorafe-ƙorafe kan illolinsa nan da can, musamman daga likitoci da sauran jami’an lafiya.
Episodes
Tsadar maganin asibiti ya tilasta wa wasu jama'a komawa amfani da gargajiya
ListenedA wannan makon shirin ya yi nazari kan yadda tsadar maganin asibiti ke tilastawa jama’a karkatawa amfani da magungunan gargajiya, kodayake akwai kiraye-kirayen masana game da illar waɗannan magunguna a mahangar likitanci. A ƙasashe irin Najeriya magungunan na gargajiya na matsayin hanyoyin neman waraka wanda aka gada tun kaka-da-kakanni kuma aka yi amanna da tasirinsu, duk kuwa da kiraye-kirayen ƙaurace masa dama ƙorafe-ƙorafe kan illolinsa nan da can, musamman daga likitoci da sauran jami’an lafiya.
Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata
ListenedShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi nazari kan matsalar birkicewar al’ada a tsakanin mata, matsala ce da ke matsayin ruwan dare a wannan zamani lura da cewa kusan dukkanin 1 cikin mata 3 akan iya samunta da wannan matsala wadda kuma ba safai aka fiya mayar da hankali akanta ba, duk kuwa da ƙalubalen hakan ga lafiyar mata. Mata da dama ne dai suka shafe shekaru suna fama da matsalolin da suka shafi al’ada amma ba tare da samun waraka ba, hakan ya sanya yawaitar ƙorafe-ƙorafe nan da can. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya
ListenedA wannan makon shirin ya yi duba kan cutar Diptheria, ko kuma mashaƙo, cutar da a baya-bayan nan ake yawan ganin ɓarkewar annobarta a wasu sassa na jihohin Najeriya wadda kuma ke kisan ɗimbin mutane baya ga kwantar da dama a asibitoci, inda wasu alƙaluma ke cewa daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar nan mutane dubu 16 da 997 suka kamu da cutar a sassan Najeriya. Masana sun yi ittifaƙin cewar mashaƙo ko kuma Deptheria tafi shafar yaran da ba a yiwa rigakafin cutuka ba ƴan shekara 1 zuwa 14 kodayake a wasu lokutan akan samu hatta waɗanda aka yiwa rigakafin sun kamu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Rawar da Ungozomar gargajiya ke takawa wajen ceton rai a yankunan karkara
ListenedGoyon ciki da haihuwa na cikin mayan ƙalubalen Lafiyar da suka addabi ƙasashe masu tasowa irin Najeriya, ta yadda a kowacce rana ake ganin mutuwar ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko kuma renon ciki, baya ga tarin jarirai da ke rasa ransu. A irin wannan yanayi galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
Lafiya Jarice: Muhimmancin tazarar haihuwa ga lafiyar uwa da jaririnta
ListenedBisa ga zubin halittar ɗan adam kowacce mace kan iya haihuwa aƙalla sau 15 zuwa 30 a tsawon rayuwarta, a wani yanayi da ƙasashen Afrika ke sahun gaba wajen yawan haihuwar, kodayake liktoci na jan hankali game da muhimmancin bayar da tazara ko kuma hutu koma taƙaita haihuwar baki ɗaya saboda dalilai na lafiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.